HANYOYiN TARBIYA(5)
5.Girmama yaro da tausaya masa: Daga cikin hanyoyin da ya kamata ka bi don samar da yaro mai tarbiya shi ne girmama yaro da tausaya masa,saboda ta wannan hanyar ce za ka samar da yaro mai farin ciki da walwala. Yaronka yana bukatar girmamawarka da nuna masa soyayyarka,kada mu ga cewa ai mu muka haife shi don haka shi bawa ne a wurinmu sai yanda muka ga dama muke juyar da shi,aa shi ma yana da hakki a kan raayinsa kamar yanda hadisi ya zo daga Sahl bn Saad Assaady yana ba mu labari wata rana an kawo wa Annabi (SAW) abun sha sai ya sha daga wannan abun shan to kuma a hannun damansa wani yaro ne a zaune a gefen hannun hagunsa kuma manya ne a zaune cikinsu har da su sayyidina Abubakar da Umar sai Annabi (SAW) ya nemi izinin yaron da ke hannun damansa ya ce masa ko za ka yi min izini in fara bawa manyan nan su sha sai yaron ya ce: aa ban yarda ba, wallahi ba zai yiwu in fifita wani a kai na ba game da kai ya rasullallah(yaron yana son ya kafa bakinsa daidai inda Annabi ya kafa bakinsa ...