HANYOYiN TARBIYA(5)

5.Girmama yaro da tausaya masa: Daga cikin hanyoyin da ya kamata ka bi don samar da yaro mai tarbiya shi ne girmama yaro da tausaya masa,saboda ta wannan hanyar ce za ka samar da yaro mai farin ciki da walwala. Yaronka yana bukatar girmamawarka da nuna masa soyayyarka,kada mu ga cewa ai mu muka haife shi don haka shi bawa ne a wurinmu sai yanda muka ga dama muke juyar da shi,aa shi ma yana da hakki a kan raayinsa kamar yanda hadisi ya zo daga Sahl bn Saad Assaady yana ba mu labari wata rana an kawo wa Annabi (SAW) abun  sha sai ya sha daga wannan abun shan to kuma a hannun damansa wani yaro ne a zaune a gefen hannun hagunsa kuma manya ne a zaune cikinsu har da su sayyidina Abubakar da Umar sai Annabi (SAW) ya nemi izinin yaron da ke hannun damansa ya ce masa ko za ka yi min izini in fara bawa manyan nan su sha sai yaron ya ce: aa ban yarda ba, wallahi ba zai yiwu in fifita wani a kai na ba game da kai ya rasullallah(yaron yana son ya kafa bakinsa daidai inda Annabi ya kafa bakinsa kuma idan aka fara ba wa manyan zai rasa wannan falalar), Annabi kuma bai yi fushi ba kuma bai yi wa yaron fada ba kawai sai ya ba shi ya fara sha tunda hakkinsa ne shi ne ya fi cancanta(a musulunci wanda yake hannun damanka shi ya fi chanchanta a kan komai a wurinka). Anan mun ga cewa Annabi ya kula da abubuwa guda biu ya kiyaye hakkin yaro na girmama shi ya nemi izininsa sannan kuma ya kiyaye hakkin manya ya nemi yaro ya musu izini tunda su manyasa ne. Da wannan ne muke iya cewa kai mai tarbiya dole ne ka rika kula da yanda za ka yi muamala da yaronka ta hanyar sanin yanda za ka yi masa magana in kana bukatar wani abu daga wurinsa kamar yanda muka ga Annabin rahma (SAW) ya yi. Kokarin kula da rashin yi masa tsawa da hantararsa a kan kuskure da ya yi ya kamata in za ka masa fada ka kula da feelings na shi saboda wulakantashi da z da zaginsa da za ka yi zai iya yi masa tasiri a rayuwa har girmansa. Don haka iyaye a kula saboda babban hadafinmu shi ne samar da yara masu cikakkiyar tarbiya da nagarta.
Akwai kaida da muke da ita a cikin addinin musulunci wacce ta zo a cikin hadisin Abu Huraira da Annabi(SAW) yake cewa:"ليس منا من لا يوقر كبيرنا ويرحم صغيرنا".  fassara " baya daga cikinmu wanda ba ya girmama manyanmu kuma ba ya tausayin kanananmu.". Wannan hadisin yana nuna mana cewa tausayin yaro yana daga cikin addinin musulunci shi ya sa Annabi ya ce ba ya daga cikinmu wato mu musulmi.
Mu sani cewa ko yaushe yaranmu suna kwaikwayo ne daga wurinmu don haka idan yaronmu ya lura da yanda muke ba shi girma kuma muna tausaya masa shi ma haka zai tashi yana girmama mutane kuma yana tausayawa kananansa. Allah ya ba mu iko. Mu hadu a fitowa ta gaba In sha Allah.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN TARBIYA(1)

HANYOYIN TARBIYA(4)

HANYOYIN TARBIYA(3)