HANYOYIN TARBIYA(3)

2. Ba wa yaro nagartaccen ilimi:
Allah madaukakin sarki a cikin kuraninsa mai tsalki yana cewa"هل يستوي الذين يعلمون والذين لا يعلمون" fassara "shin wadanda suke da  ilimi suna dai dai da wadanda ba su da shi" tabbas ba za su yi daidai ba. Ilimi shi ne mabudin rayuwa duk girman mutum da hankalinsa in ba ya da ilimi za ka ga yana da nakasu(tawaya). To shi ya sa kai me tarbiya za ka jajirce don dora yaronka akan hanyar neman ilimi tun yana karami. Ka samar mishi makaranta ta kwarai wacce take bada nagartaccen ilimi da nagartacciyar tarbiya. Dole ne ka kula da hannun wa za ka danka yaronka. Wasu iyaye saboda kwadayin yaro ya koyi turanci za ka ga sun kai shi makarantar arna inda baa ma kula da addini ba balantana kuma tarbiyarsa.koyon yare irin turanci da wasu yaruka yana da babban amfani ga mutum kamar yanda Annabi (SAW) ya kwadaitar amma sai mutum ya bi ta hanyar da ta dace wacce zai kare yaronsa daga koyon wata akida wacce ba ta dace da akidar musulunci ba.
  Ilimin addinin musulunci shi ne kan gaba wurin koyo kafin kowane ilimi,saboda da shi ne mutum zai san hadafin halittarsa da kuma aikata abunda yake shi ne hadafin halittar ta sa kamar yanda kurani ya yi bayani:"وماخلقت الجن والانس الا ليعبدون" fassara"ban halicci mutum da Aljani ba sai don su yi bauta". Bautar Allah shi ne dalilin halittar dan adam. Kuma bautar nan ba yanda ka ga dama za ka yi ta ba dole sai ta hanyar ilimin addini za ka san yanda Allah ya ce a bauta masa. Shi ya sa ya zama wajibi gare ka kai mai tarbiya ka fara koyawa yaronka karatun kurani da haddarsa haka hadisan Annabi (SAW),ilimin fikhu ,tauhidi,da dai sauran ilimuka da suke karantar da addinin musulunci.
  Akwai iyayen da ba sa kula da karatun addini su a karan kansu ballantana ma su koyar da 'ya'yansu ko kuma su kai su inda za su koya,har ma suna ganin masu karatun addini ba su waye ba,to gaskiya wannan gurguwar fahimta ce ya kamata su sani cewa duk wani ilimi yana bayan na addini ne. Su sani cewa Allah madaukakin sarki cewa ya yi "يايها الذين ءامنو قوا انفسكم واهليكم نارا" fassara "ya ku wadanda kuka yi imani,lallai ku kare kanku da iyalanku daga wuta". 'Ya'ya kuwa suna cikin iyalai,to ta yaya za ka kare iyalanka daga wuta idan ba ka san yanda Allah ya ce a bauta masa ba. Sannan shi ilimin addini shi ne wayeya don shi ne ya kunshi rayuwa ya karantar da su yanda za su yi rayuwarsu gaba daya. Allah madaukakin sarki shi ya halicci dan adam don haka shi ya san rayuwar da tafi dacewa da shi sai ya tsara masa ita daidai da shi,ya kuma yi umurni da bin dokokin da ya shata don gudanar da wannan rayuwar da ya tsara masa,to kuma kai kana ganin cewa duk mai bin wannan addinin bai waye ba,to anan Allah ne kake ja da shi don haka iyaye a kula sosai.
  Bayan ilimin addini shi ne kowane irin ilimi zai biyo baya in dai mai amfani ne don addini musulunci ya umurce mu da haka din.shi ya sa za ka yi kokarin ganin cewa yaronka ya samu kyakkyawan ilimi na zamani wanda zai ba shi damar samun ingantacciyar rayuwa a can gaba,amma fa kada a yarda a dasa wa yaro cewa wannan shi ne hadafin kawai ya kamata a gwamawa yaro cewa neman ilimi kowane iri ne ibada ne don haka zai fahimci cewa hatta ilimin zamani da yake karanta don neman abinci shi ma ibada ne wannan zai masa tasiri sosai zai kuma sa ya himmantu da abun kuma ba zai rika algussu ko wani abu mai kama da haka ba.
Wasu Nasihohi da za su taimaka wurin dasa son neman ilimi a wurin yaro:
1. Yawan ambaton falalar ilimi da girmama littatafai da malamai a gaban yaro saboda ya siffantu da wannan sifar.
2.kebancewa yaro wurin karatu a gida da shirya shi gwargwadon hali don samar masa yanayi mai kyau na karatu.
3.kokarin sayawa yaro litatafai na shi na kanshi tare da kula da zabin yaro wurin sayen litatafan.
4.yi masa library(wurin aje litatafai) ko da kuwa da kwalin indomie ne zaa iya gyara shi a kawata shi ya sa littaffansa in ba halin sayen drower ta littafai
5.koya masa asusu don sayen littafin da yake bukata don haifar da dabiar sayen littatafai don karuwa bayan ya girma.
Mu hadu a fitowa ta gaba in sha Allah.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN TARBIYA(1)

HANYOYIN TARBIYA(4)