HANYOYIN TARBIYA(4)
3.Tarbiyantar da yaro a kan kyawawan halaye:
Lallai tarbiyantar da yaro a kan dabiu na kwarai yana daga cikin abunda addinin musulunci ya yi umurni da shi saboda muhimmancin hakan ga mutum da kuma rayuwar alumma. Samar da 'ya'ya na gari ya kan samar da ci gaba ga alumma da kuma samun makoma mai kyau ga wanda ya sifantu da su. Siffantuwa da kyawawan halaye abu ne mai girma wanda dalilin hakan Allah madaukakin sarki ya yabi Annabinsa(SAW) a kuraninsa mai tsalki inda yake cewa:"وانك لعلى خلق عظيم"fassara "lallai kana a kan halaye masu girma" wato kyawawan halaye. Haka Annabi(SAW) yana cewa a cikin hadisi:"بعثت لأتمم مكارم الاخلاق" fassara "an aiko ni don in cika kyawawan halaye". Wato kyawawan dabiu su ne babban sakon da musulunci yake dauke da shi. Shi ya sa yake daga cikin alamar musulmi na kwarai siffantuwa da halaye na kwarai. Addinin musulunci gaba dayan shi yana misaltuwa ne a cikin kyawawan dabiu kuma imani kansa yana bayyna ta hanyarsu kamar yanda Annabi(SAW) yake cewa:"اكمل المؤمنين ايمانا احسنهم خلقا" fassara "mafi kamala(cika) a cikin muminai shi ne wanda ya fisu kyawawan dabiu". Mun ga cewa siffantuwa da dabiu na kwarai alama ce ta cikar imani. Wannan zai ba mu kwarin guiwar jajircewa wurin samar da iri mai dauke da halaye na kwarai domin duk sanda aka samar da irin wannan iri shi zai sa alumma ta cika da masu kamalallen imani da za su ciyar da ita gaba,yawan masu munanan dabiu a cikin alumma ya kan rusa ta ne,kuma maauni ne na auna alumma.
Amma ta wace hanya ce kai mai tarbiya kake ganin za ka iya samar da wannan irin da ya siffantu da dabiu masu kyau. Ga kadan daga cikin hanyoyin.
1. Mai tarbiya shi ma dole ne ya siffantu da dabiu na kwarai in dai yana son yaran shi su siffantu da wadannan dabiun. Don ba zai yiwu kana kokarin koyar da yaronka zama mai gaskiya ba amma kuma kai kana yin karya. Domin kuwa yaro a dabiarsa yana kwaikwayon abun da manyansa suke yi.
2. Kokarin sa yaro yin abunda kake tarbiyyarsa a kansa na kyawawan dabiu. Misali kuna cikin tafiya kai da yaronka ka mika masa kudi don bawa wani mabukaci ka ga nan zai koyi tausayi da kuma sadaka. Ko kuma kuna cikin tafiya kuka ga kaya ko wani abu mai cutarwa a kan hanya sai ka ce masa duke wancan abun ka jefa a gefen hanya kar ya cutar da mutane. Ka ga nan zai fahimci ashe baa barin abu mai cutarwa a kan hanya saboda kar ya cutar da mutane. Da haka zai koyi dabiu masu yawa kuma su zauna a kwakwalwarsa.
3.kokarin yi masa nasiha akan dabiu na kwarai da karanto masa ayoyi da hadisai da suke bayani a kan su da sakamakon wanda suka siffantu da su. Sai dai ya kasance a cikin hikima da kula da hankalin yaro da shekarun sa.
4.kwadaitar da shi a kan dabiun kwarai da kuma tsoratar da shi a kan munanan dabiu,kwadaitar da shi da abubuwan da za su taimaka mishi da siffantuwa da dabiun kwarai. Saboda matsayin shi na yaro yana bukatar haka din,misali idan ya fadi gaskiya a kan wani abu da aka tambaye shi sai ka rungume shi ka sumbance shi wannan zai ba shi karfi wurin tsare gaskiya saboda tasirin abunda ka masa sakamakon gaskiyar da ya fada. Haka duk wani abu na alkhairi da ya yi ka nuna masa farin cikinka da yaba masa,amma ba a cika son ka koya masa ba shi kudi ko wani abu mai kama da haka ba. Haka ma tsoratar da shi ta hanyar hana shi yin wata wasa da yake son yi ko kin tafiya da shi wani wuri da yake son zuwa da dai irin abubuwan da za su dan sosa masa rai amma fa ba ma su cutar da shi ba irin su duka da zagi da kwatsewa da izgilanci gare shi don wannan ya kan bata masa rayuwa ya kuma hana shi yin abunda ake so ya yi din. Akwai lokacin da zaa dake shi amma in an jaraba duk hanyoyin da suka dace kamar yanda Annabi (SAW) ya yi umurni da adaki yaro in ya kai shekara goma ba ya sallah. Amma mu lura dukan sai da ya kai wata manzila ta gane maanar dukan.
5. Koyar da shi kyawawan dabiu ta hanyar labarta masa kissoshi masu maana wadanda suke dauke da sakon da kake so ka isar masa. Saboda kissa tana tasiri sosai ga yaro kuma tana taimakawa wurin isar da sako ta hanyar da ta dace da yaro. Amma fa a kula ba ko wace kissa za ka labartawa yaronka ba dole sai ka tace ka rairaye sannan ka gabatar masa da ita.
Mu hadu a fitowa ta gaba in sha Allah.

Comments
Post a Comment