HANYOYIN TARBIYA(1)
HANYOYIN DA SUKA DACE KA DORA YARONKA AKANSU DON KYUTATA TARBIYARSA
- DASA SHI A KAN AKIDA TA KWARAI:
Fassara:”ba wani yaro da ake haihuwa face yana akan fidrah(akidah ta kwarai) sai dai iyayensa su maida shi bayahude ko kirista ko bamaguje”
Da wannan hadisi ne nake cewa ya kai mai tarbiya dole ne ka jajirce wurin kiyaye wannan fidrah da yaro ya akanta,don idan ka yi sake har ya fada zuwa ga wata mummunar akidah to lallai Allah zai tambaye ka ranar lahira. Annabi(SAW) yana cewa:”كلكم راع وكلكم مسؤول عن رعيته”
Fassara:”dukkaninku makiyaya ne kuma kowannenku zaa tambaye shi akan abun kiwonsa”.
Wace hanya ce ya kamata ka bi kai mai tarbiya don dasa yaronka a kan akida ta kwarai?
Tun farko dai ya wajaba samo masa uwar kwarai wacce ta ginu akan karantarwa ta addini sannan kuma ta koshi da akida ta kwarai
Dole ne kiyaye ladubban kwanciya(jimaii) da gabatar da shi akan karantarwa ta addini. Sannan ki sani ya ke uwa bayan samun cikin yaronki dole ne ki kiyaye abubuwa da dama domin yaro tun yana ciki ake cusa masa akidah ta kwarai,domin kuwa idan kika kasance duk motsinki akan abunda yake yardar Allah ne to lallai yaronki zai tasirantu da haka. Misali idan kika kasance zuciyarki ta rataya da kurani da ibada da yawan Zikiri to lallai wannan zai yi tasiri ga yaronki. Haka ma idan zuciyarki ta rataya ga son kide kide da bushe bushe da son abubuwan banza to haka ma yaron zai tasirantu da haka din. Don haka dole ne lokacin da uwa take da ciki ta kula kuma ta yi takatsantsan.
Bayan haihuwar yaro Annabi (SAW) ya umurce mu da fara yiwa yaro kiran sallah a kunnensa na dama da yi masa ikama a kunnensa na hagu. Wannan yana nuna mana cewa abu na farko da ake so yaro ya fara ji a kunnensa shi ne kalmar tauhidi mun kuma sani cewa kiran sallah da ikama suna kunshe da kalmar tauhidi.
Daga nan kuma uwa ta ci gaba da kiyayewa wurin muamala da yaro a wannan marhala ta jarintaka,ta kasance duk lokacin da za ta shayar da shi ta ambaci bismillah haka ma in za ta dauke shi da dai sauran irin wadannan abubuwa. Ana son ya saba da jin ambaton Allah tun yana jinjiri.’yar uwa kar ki ce ai ba ya fahimta aa ki yi kokarin yi saboda tarbiyar yaronki kuma haka addinin musulunci ya koyar da mu.
Bayan yaro ya yi wayo ki yi kokarin rataya zuciyar shi ga son Allah ta hanyar nuna masa irin niimomin da Allah ya yi mana,yayin da za ki rinka fahimtar da shi Allah ne yake ba mu abinci,kayan wasa,da dai sauran niimomin da Allah ya yi mana,domin shi yaro a dabiarsa yana son wanda yake kyautata masa,to idan ya gane cewa duk wata niima daga wurin Allah ta ke zowa to zuciyarsa za ta rataya ga son Allah.
Idan aka yi nasara a kan tabbatar da son Allah a zuciyar yaro to kuwa zai tashi da son duk wani umurni da Allah ya yi umurni da shi da kuma hanuwa da duk wani abu da Allah ya yi hani da shi,saboda a dabiar dan adam idan yana son mutum zai rika jin maganarsa to haka ma yaro zai kasance game da ubangijinsa.
Daga nan kuma mai tarbiya zai yi kokarin ganin cewa ya koya wa yaronsa jin tsoron Allah a bayyane ko asirce,ya fahimtar da shi cewa Allah yana kallonsa a dukkanin alamurransa wannan kuwa zai kasance ne ta hanyar hikayanta masa kissoshi da suke dauke da wannan darasin da yi masa sharhi akan ayoyi da hadisai da suke magana akan haka amma fa gwargwadon hankalinsa. Da haka yaro zai tashi yana jin kunyar aikata sabo a bayyane ne ko a boye don ya fahimci duk daya ne koma ya buya ko ya yi a bayyane,Allah dai yana ganinsa.
Haka kuma kokarin koya wa yaro komawa ga Allah lokacin tsanani ne ko na jin dadi,wannan kuwa zai samu ne ta hanyar da zai ganka kana yin haka din idan abu ya same ku na bakin ciki zai ga kun koma ga Allah ta hanyar addua da hakuri ko na jin dadi ta hanyar hamdala da yabon Allah. Sai kuma koya wa yaro azkar don neman kariya daga wurin Allah a lokacin da ya shiga wahala da damuwa. Duk wadannan suna karkashin dasa yaro a kan akida ta kwarai.
Idan aka yi nasara wurin tabbatar da imani a cikin zuciyar yaro da kuma dora shi a kan akida ta kwarai kamar yanda aka yi bayani a sama to kuma sai kokarin koya masa yanda zai kyautata alakar sa da ubangiji ta hanyar kiyaye ibadarsa kamar sallah azumi karatun kurani da dai sauransu.
Don haka kai mai tarbiya sai ka dage wurin dasa kyakkyawar akida ga yaronka don samun iri na gari da zai zama cikin wadanda Annabi(SAW) zai yi alfahari da su ranar kiyama.
Mai karatu biyo ni a hankali don ci gaba akan yanda za ka dasa akidar kwarai ga yaronka
Comments
Post a Comment