GUZURIN MAI TARBIYA
Sannanen abu ne cewa duk wanda zai yi tafiya dole ne ya tanadi guzuri in dai yana son tafiyar ta yi nasara,to haka ma tarbiya tafiya ce da take bukatar guzuri don cimma manufa. GUZURI NA FARKO:TSARKAKE NIYYA, addinin musulunci ya umurce mu da kyautata niyya ga duk wata ibada da mutum yake kokarin aikatawa,haka ma tarbiya ita ma ibada ce dole ne ka tsarkake niyyarka da neman lada a wurin Allah a kan kokarin da kake yi na ganin cewa yaranka sun tashi a kan tarbiya ta kwarai. To idan har ka tsarkake niyyarka Allah ba zai tambaye ka ba a kan rashin shiriyarsu ko wani zunubi da suke aikatawa Allah madaukakin sarki ya ce:"يايها الذين آمنوا عليكم انفسكم لا يضركم من ضل اذاهتديتم" fassara "ya ku wadanda kuka yi imani ku kula da kanku rashin shiryuwar wasu ba zai cutar da ku ba" wato in dai har kun yi iya kokarinku kuma kun bi duk hanyoyin da suka dace,to tsalkake niyya yana cikin bin hanyoyin da suka da ce wurin shiriyar yara. Kada ka rika tunanin tarbiyar nan da kake yi ...