GUZURIN MAI TARBIYA

Sannanen abu ne cewa duk wanda zai yi tafiya dole ne ya tanadi guzuri in dai yana son tafiyar ta yi nasara,to haka ma tarbiya tafiya ce da take bukatar guzuri don cimma manufa.
GUZURI NA FARKO:TSARKAKE NIYYA, addinin musulunci ya umurce mu da kyautata niyya ga duk wata ibada da mutum yake kokarin aikatawa,haka ma tarbiya ita ma ibada ce dole ne ka tsarkake niyyarka da neman lada a wurin Allah a kan kokarin da kake yi na ganin cewa yaranka sun tashi a kan tarbiya ta kwarai. To idan har ka tsarkake niyyarka Allah ba zai tambaye ka ba a kan rashin shiriyarsu ko wani zunubi da suke aikatawa Allah madaukakin sarki ya ce:"يايها الذين آمنوا عليكم انفسكم لا يضركم من ضل اذاهتديتم" fassara "ya ku wadanda kuka yi imani ku kula da kanku rashin shiryuwar wasu ba zai cutar da ku ba" wato in dai har kun yi iya kokarinku kuma kun bi duk hanyoyin da suka dace,to tsalkake niyya yana cikin bin hanyoyin da suka da ce wurin shiriyar yara.
Kada ka rika tunanin tarbiyar nan da kake yi  wahala ce kawai kake yi,kokuma ka sa babban hadafinka shi ne kawai kana yi ne don  in yaran sun girama su taimaka maka,aa ka sa a zuciyarka cewa wannan aiki ne na ibada kuma Allah ne ya dora maka shi don haka duk abunda kake yi a kan yaranka saboda shi kake yi kuma a wurin shi kake neman sakayya. Wannan guzuri ne babba da zai taimaka maka kuma ba zai bari ka kasa ba wato ka ji ka gaji koda kuwa kana ga cewa yaran ba sa kan abunda kake dora su a kan shi.
GUZURI NA BIU:TSORON ALLAH DA ZAMA NA GARI :duk abunda mutum ya sa tsoron Allah a kansa Allah yana shige masa gaba Allah madaukakin sarki ya ce:"ومن يتق الله يجعل له مخرجا ويرزقه من حيث لا يحتسب"fassara "duk wanda ya ji tsoron Allah zai samar masa mafita kuma ya azurta shi ta inda ba ya tsammani" wanna ya nuna mana duk abunda ka sa Allah a gaba kuma ka ji tsoronsa a cikinsa to lalle Allah zai taimakae ka ya kuma ba ka abun nan ta inda baka tsammani. Ka ga lokacin da kake tarbiyar yaranka ka sa Allah gaba game da yaran nan to Allah zai taimake ka a kan tarbiyarka ya kuma ba ka 'ya'ya na gari.
GUZURI NA UKU:HAKURI,Tarbiya babban alamari ce kuma tana da wahala,saboda haka ake son mai tarbiya ya yi guzurin hakuri don shi ne zai taimaka masa wurin iya ci gaba da naciya a kan tarbiyar da yake yi. Sannan kuma idan ya yi hakuri har wa yau Allah zai kasance tare da shi kamar yandaya fada a cikin Quraninsa mai tsarki "ان الله مع الصابرين" fassara "lallai Allah yana tare da masu hakuri".
Don haka masu tarbiya a jure a yi hakuri a daina saurin fushi har ana tsinewa yara saboda Allah ya kasance tare da ku domin samun nasara a cikin tarbiyar yaranku.
GUZURI NA HUDU: ILIMI,neman ilimi wajibi ne a kan kowane musulmi kamar yanda hadisi ya zo "طلب العلم فريضة علي كل مسلم و مسلمة" fassara "neman ilimi wajibi ne ga kowane musulmi da musulma. Don haka mai tarbiya dole ne ya tashi ya nemi ililmi tukuru na addini da na boko,addinin musulunci ya koyar da mu yanda za mu yi tarbiyar 'ya'yanmu tun daga haihuwarsu har zuwa lokacin da nauyinsu ya sauka kanmu, to idan ba ka yi karatun addini ba ta yaya za ka dora yaronka akan akida ta kwarai kamar yanda muka yi bayani a cikin hanyoyin tarbiya,haka ma ibadarsa da dai sauran abunda ya kunshi addini. 'Yan uwa masu tarbiya islamiya kadai ba ta isa dole sai iyaye sun taimaka saboda ba tsuran karatu kadai yaranmu suke bukata ba aa suna bukatar ilimi da aiki a aikace,don haka mun ga kenan akwai bukatuwar ilimin addini mai zurfi.
Ilimin boko kuwa yana taimakawa mai tarbiya wurin fahimtar da yaronsa duniya da halin rayuwa da kuma iya gina kai da dogaro da ita,iyaye marasa ilimin boko za ka ga suna samun matsala wurin fahimtar halin rayuwa da canje canjen zamani wannan kuma yakan yi musu tasiri wurin tarbiyar yaransu,don haka masu tarbiya ayi kokari ko ba ayi karatun boko tun ana kanana ayi yaki da jahilci. Koyaushe musulunci yana bukatar kammalallen mutum duk inda aka kwankwasa aji ba laifi.
Sai abu na gaba shi ne ya kamata mai tarbiya ya zama mai yawan karance karance da bincike a kan duk wani abu da masana suke fada ko rubutawa a kan tarbiya saboda kara fahimtar yanda ake tarbiya ta kowane bangare don faidantuwa da hakan.
GUZURI NA BIYAR:ADDUA, kamar yanda muka sani cewa addua babban guzuri ce ga komai ballantana kuma a fagen tarbiya,kuma makamin mumini ce kamar yanda hadisi ya zo,"الدعاء سلاح المؤمن" addua makamin mumini ce. To ya zama dole mai tarbiya ya dage da yiwa yaransa addua  saboda nemar musu shiriya da dacewa. Allah madaukakin sarki yana cewa:" وقال ربكم ادعوني استجب لكم" fassara "kuma ubangijinku ya ce ku roke ni in karba muku". Adduar iyaye ga 'ya'yansu karbabbiya ce Annabi(SAW) ya ce: “ثلاث دعوات يستجاب لهن لا شك فيهن: دعوة المظلوم ودعوة المسافر ودعوة الوالد لوده" fassara " Adduoi guda uku ba makawa Allah yana amsawa wanda ya yi su: adduar wanda aka zalunta,da adduar matafiyi,da adduar iyaye ga 'ya'yansu". Don haka ake son kullun adduar iyaye ta zama ta alheri ga 'ya'yansu,ba a son kana yiwa 'ya'yanka mummunan lafazi da laana saboda gudun karbuwar hakan a wurin Allah. Don haka 'yan uwa mu dage da yiwa 'ya'yanmu addua don guzuri ne babba a fagen tarbiya. Mu hadua fitowa ta gaba Insha Allah.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN TARBIYA(1)

HANYOYIN TARBIYA(4)

HANYOYIN TARBIYA(3)