MU NE MUKA JAWO LALACEWR YAYANMU KO ZAMNI
Mun dauka ita tarbiya shi ne a cewa yaro yi ya yi ace ya bari ya bari,wannan kuwa juzui ne na tarbiya wanda ake cinma sa idan aka bi hanyoyin da suka dace. Amma matsalarmu muna cinma wannan juzui da karfin tsiya a daidai lokacin da mun kashe tunanin yaro, mun halaka kwakwalwarsa,mun yaki yancinsa sai ya tashi cikin tsoro da rashin walwala,a cikin wannan yanayi da yaro yake cikinsa mu kuma muna murna mun yi wa yaronmu tarbiya tunda in mun ce ya yi zai yi in mun ce ya bari zai bari, shin muna tunanin wannan kuwa ba naui ne na son kai ba? Mu sani cewa yaro yana da tunani irin na sa,ya na da hankali irin na sa,komai karancinsa,yaro yana da zabi don haka ya kamata ace yana da yanci gwargwadon hankalinsa,kawai mu abunda Allah ya dora mana mu yi kokarin dora shi a kan hanyar da ta da ce da fadakar da shi ta hanyoyin da suka dace. To amma ya ya za ka san wadannan hanyoyin da suka dace,idan muka tashi muka nemi ilimin tarbiyar yara a cikin karance karancenmu domin kuwa a cikinsu ne za mu...