MU NE MUKA JAWO LALACEWR YAYANMU KO ZAMNI

Mun dauka ita tarbiya shi ne a cewa yaro yi ya yi ace ya bari ya bari,wannan kuwa juzui ne na tarbiya wanda ake cinma sa idan aka bi hanyoyin da suka dace.
Amma matsalarmu muna cinma wannan juzui da karfin tsiya a daidai lokacin da mun kashe tunanin yaro, mun halaka kwakwalwarsa,mun yaki yancinsa sai ya tashi cikin tsoro da rashin walwala,a cikin wannan yanayi da yaro yake cikinsa mu kuma muna murna mun yi wa yaronmu tarbiya tunda in mun ce ya yi zai yi in mun ce ya bari zai bari, shin muna tunanin wannan kuwa ba naui ne na son kai ba?
Mu sani cewa yaro yana da tunani irin na sa,ya na da hankali irin na sa,komai karancinsa,yaro yana da zabi  don haka ya kamata ace yana da yanci gwargwadon hankalinsa,kawai mu abunda Allah ya dora mana mu yi kokarin dora shi a kan hanyar da ta da ce da fadakar da shi ta hanyoyin da suka dace. To amma ya ya za ka san wadannan hanyoyin da suka dace,idan muka tashi muka nemi ilimin tarbiyar yara a cikin karance karancenmu domin kuwa a cikinsu ne za mu fahimci ya tunanin yaro yake a kowace marhala ta rayuwarsa ya yake fahimtar abubuwa me yake bukata ako wace marhala da dai sauransu.
Mun san cewa akwai tabarbarewar tarbiyar yara a wannan zamani,kuma sai muna ta zargin yara da zamani har ma muna cewa yaran zamani ba za ka iya musu ba. Mu matsayinmu na iyaye ma su tarbiyar yaran ba mu zargi kanmu ba a kan shin ba ko mu ne muke da laifin tabarbarewar tarbiyar wadannan yaran ba;bayan mun tabbatar da ya zo a hadisi cewa shi yaro ana haihuwarsa alhali zuciyarsa tana fari fat kamar farar takarda sai dai iyayensa ne suke karkatar da shi a kan fidirar da ya zo da ita,mun kuwa ga kenan duk abunda ya dasu a zuciyar yaro daga iyayensa ne da alummar da ke tarbiyarsa suka dasa shi. Don haka iyaye kowa ya bibiyi kansa ya fahimci ya ake tarbiyar yara ya kuma komawa litatafai da sirar Annabi SAW don ceto wadannan yaran da muke zargin tabarbarewar tarbiyarsu,alhakinsu yan rataye a kanmu kuma Allah zai tambaye mu.
Mu hadu a fitowa ta gaba In sha Allah.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN TARBIYA(1)

HANYOYIN TARBIYA(4)

HANYOYIN TARBIYA(3)