Posts

Showing posts from June, 2020

KYAKKYAWAR MUAMALA BABBAR MU'UJIZA CE A WURIN TARBIYA

Kyayyawar muamalar da kake yi wa 'ya'yanka/ki tana haifar da babban alamari wurin tarbiyarsu, domin ita ce za ta taimaka wurin gina kyakkyawar alaka tasakaninka/ki da su. Malaman tarbiya sun tabbatar da cewa kashi 70 cikin 100 na rassan da ake concentrating a kansu wurin tarbiya ya tattara ne a cikin kulla kyakkyawar alaka tsakanin iyaye da 'ya'yansu. Duk lokacin da alaka ta yi rauni tsakanin iyaye da 'ya'yansu duk lokacin da aka samu matsala a wurin tarbiya. Mafi yawan matsalolin tarbiya da suke faruwa a alumma sakamako ne na raunin alaka tsakanin iyaye da 'ya'ya. Idan ka kyautata muamalarka ga 'ya'yanka lokacin ne za su fi mutuntaka kuma su daukeka mutumen kirki, ganin cewa  mutumen kirki ne a idonsu shi zai sa ka ga duk wani abu na kirki da ka ke yi suna kokarin koyi da kai a kansa. Idan kuma ka munana muamalarka gare su za ka ga suna gudunka kuma ba sa mutuntaka, koda kuwa ka ga mutuntuwa to a gaban idanunka ne a bayanka za ka sha mamaki...