KYAKKYAWAR MUAMALA BABBAR MU'UJIZA CE A WURIN TARBIYA


Kyayyawar muamalar da kake yi wa 'ya'yanka/ki tana haifar da babban alamari wurin tarbiyarsu, domin ita ce za ta taimaka wurin gina kyakkyawar alaka tasakaninka/ki da su.
Malaman tarbiya sun tabbatar da cewa kashi 70 cikin 100 na rassan da ake concentrating a kansu wurin tarbiya ya tattara ne a cikin kulla kyakkyawar alaka tsakanin iyaye da 'ya'yansu.
Duk lokacin da alaka ta yi rauni tsakanin iyaye da 'ya'yansu duk lokacin da aka samu matsala a wurin tarbiya. Mafi yawan matsalolin tarbiya da suke faruwa a alumma sakamako ne na raunin alaka tsakanin iyaye da 'ya'ya.
Idan ka kyautata muamalarka ga 'ya'yanka lokacin ne za su fi mutuntaka kuma su daukeka mutumen kirki, ganin cewa  mutumen kirki ne a idonsu shi zai sa ka ga duk wani abu na kirki da ka ke yi suna kokarin koyi da kai a kansa.
Idan kuma ka munana muamalarka gare su za ka ga suna gudunka kuma ba sa mutuntaka, koda kuwa ka ga mutuntuwa to a gaban idanunka ne a bayanka za ka sha mamaki, kuma ba za ka cika musu ido ba su rika ganinka mutumen kirki  koda kuwa mutanen suna maka shedar haka.
Abunda ake so ga tarbiya, 'ya'yanka su mutuntaka su soka saboda kana burge su, dalilin burge su da kake yi za ka zama abun koyinsu. Wannan kuwa ba zai samu ba sai idan akwai kyakkyawar alaka tsakaninka da su ta hanyar muamalar da kake musu.
Akwai abubuwa da suke ruguza alaka tsakanin iyaye da 'ya'yansu:
Irin su duka, tsawa, zagi, fada, tonon asiri, tozartawa, sakaci, sangarci, wadannan abubuwa ne da in mutum ya lazimce su a tarbiyarsa ba zai ga sakamako mai kyau ba. Domin ba sa karfafa alaka tsakanin iyaye da 'ya'yansu bal ma sai dai ka ga 'ya'yan suna nesa da iyayen ba wani sirri na su da suke fada musu sai dai in ya bayyana ba da son ransu ba. Wannan tana cikin babbar matsalar da ya sa ake son iyaye su kulla alaka mai kyau tsakaninsu da 'ya'yansu su zama abokanai/kawayensu saboda sanin cikinsu da wajensu. Amma fa ka sani ba yanda zaa yi ka zama aboki/kawar 'ya'yanka alhali kana dukansu ko tozartasu da sauran abunda muka fada a baya.
Hira da yaranka, girmama su, nuna soyayyarka gare su ba tare da wani sharadi ba, jinkayinsu, yaba musu, kau da kai ga abun da bai je ya dawo ba, hakuri da su, lurar da su cikin natsuwa da girmamawa, fahimtarsu, da sauran ire iren wadannan su ne suke jawo kulluwar kyakkawar alaka da kyakkyawar muamala tsakaninka da  'ya'yanka.
Muna rokon Allah ya taimake mu ya ba mu ikon yi wa 'ya'yanmu kyakkyawar muamala don samun babban sakamako a wurin tarbiyarsu
Mu hadu a fitowa ta biu In sha Allah


Kundin Tarbiya
Fatima Bello D/malam
14/6/20

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN TARBIYA(1)

HANYOYIN TARBIYA(4)

HANYOYIN TARBIYA(3)