YARDA DA KAI(self confidence)
Yarda da kai,wata sifa ce da ya kamata iyaye su kula da ita yayin tarbiyar 'ya'yansu. Domin kuwa rashin samun wannan sifa tun yaro yana karami ya kan haifar masa da matsaloli da dama har bayan girmansa. Rashin yarda da kai shi yake sa mutum ya rika tsoron jarraba abubuwa a rayuwarsa,tsoron magana cikin mutane,yanke hukunci idan abu ya same shi,yawan raki,rashin sanin ciwon kai,guduwa a kan abunda yake ya kamata mutum ya yi. Rashin yarda da kai ne yake sa mutum ya rika jin yana da nakasu,sai ya yi ta kokarin boye nakasin na sa da wasu abubuwa,shi ya sa kullun tunaninsa kar mutane su ce ya yi kaza,ko bai yi kaza ba. To wannan duk rashin samun sifar yarda da kai ne tun yaro yana karaminsa. Kadan daga cikin hanyoyin da suke gina sifar yarda da kai a wurin yaro lokacin da ake tarbiyarsa a shekarunsa na farko na rayuwarsa,domin gina rayuwar mutum tana dogara ne akan yanda aka yi muamala da shi lokacin yarinta. 1. Bawa yaro zabi akan abubuwan da suka shafi rayuwarsa,misali wata r...