KATSAWA YARO TSAWA HAR YA FIRGITA DA MUGUN DUKA BA FANNIN TARBIYA NE BA
Katsawa yaro tsawa har ya firgita da mugun duka ba za su sa yaro ya zama mai jin magana ba ko mai daa sai dai su sa ya zama matsoraci,makaryaci,firgitacce.
Matsoraci:saboda duk abunda ake hana shi zai bar shi ne saboda tsoro ba wai saboda ya yarda da abunda yake yi ba dai dai ne ba. Shi ya sa za ki ga idan kina kusa ba zai yi abunda kike hana shi ba amma da kin daga zai aikata saboda lokacin da ya yi kuskuren ba ki kwantar da hankalinki kin natsu kin fahimtar da shi wannan abun da yake yi kuskure ne ba. Da yawa akan daki yaro ba tare da ya san me ya sa aka dake shi ba, kawai zai ji cewa kawai baa son ya yi abun ne kawai,amma da kin fahimtar da shi a kwanciyar hankali tare da nuna masa bacin ranki ko fushin Allah akan wannan kuskuren da zai fi ganewa. In ma ta kama ki kirkiri labari wanda ba karya a cikinsa da yake nuna rashin kyaun kuskurensa da zai fi tasiri a kan tsawa da duka.
Makaryaci:saboda tsoron duka da tsawa sai yaronki ya yi abu ki tambaye shi sai ya ce miki ba shi ya yi ba kuma alhali shi ya yi. Saboda ya san ba ki da wani uslubi na gyara sai duka,don haka sai ya fadi karya. Kin ga nan kin koya masa karya ba tare da kin sani ba.
Firgitacce:yaronki zai zama bai da natsuwa,kullun a firgice yake, idan wata matsala ta same shi tsakaninsa da abokanensa ba zai iya warware ta a natse ba sai dai ka ji shi yana ihu da tsawa da kai duka saboda haka ya ga mahaifiyarsa tana yi idan ta tashi warware matsalarta tsakaninta da shi.
Har ko yaushe mu abun koyi ne a wurin 'ya'yanmu,don haka ya kamata idan suka yi kuskure mu natsu mu fahimtar da su kuskurensu,mu koyar da su neman gafara da yafiya akan kuskuren,idan kuma barna ce mu nuna musu hanyar gyarawa. Mu sani yara suna fahimta komai karancinsu,kuma suna da feelings ba ya kamata mu rika muamalantarsu kamar ba mutane ba,amanarsu Allah ya ba mu.

Comments
Post a Comment