YARDA DA KAI(self confidence)
Yarda da kai,wata sifa ce da ya kamata iyaye su kula da ita yayin tarbiyar 'ya'yansu. Domin kuwa rashin samun wannan sifa tun yaro yana karami ya kan haifar masa da matsaloli da dama har bayan girmansa.
Rashin yarda da kai shi yake sa mutum ya rika tsoron jarraba abubuwa a rayuwarsa,tsoron magana cikin mutane,yanke hukunci idan abu ya same shi,yawan raki,rashin sanin ciwon kai,guduwa a kan abunda yake ya kamata mutum ya yi.
Rashin yarda da kai ne yake sa mutum ya rika jin yana da nakasu,sai ya yi ta kokarin boye nakasin na sa da wasu abubuwa,shi ya sa kullun tunaninsa kar mutane su ce ya yi kaza,ko bai yi kaza ba. To wannan duk rashin samun sifar yarda da kai ne tun yaro yana karaminsa.
Kadan daga cikin hanyoyin da suke gina sifar yarda da kai a wurin yaro lokacin da ake tarbiyarsa a shekarunsa na farko na rayuwarsa,domin gina rayuwar mutum tana dogara ne akan yanda aka yi muamala da shi lokacin yarinta.
1. Bawa yaro zabi akan abubuwan da suka shafi rayuwarsa,misali wata rana yaro yakan yi tsaye ya ce sai kaya kaza zai saka,ni kuma ba su nike so ya saka ba ,to kamata ya yi tun farko in fitar masa kamar kala uku in bashi zabi akan ya zabi daya cikin ukun nan,wannan zabin da na ba shi zai ji cewa yana da 'yanci kuma yana da kima,wanda hakan zai sa masa farin ciki da alfahari da kansa da kore masa jin yana da nakasu.
Wannan yana shiga har wurin karatun yaro musamman lokacin da ya mallaki hankalinsa,zai shiga jamia ka ba shi zabi a kan abunda yake so ya karanta, so da yawa yaro yana son ya karanta wani fanni iyaye su yi tsaye su ce sai fannin da suka zabar masa,wannan sam ba daidai ba ne kuma rashin sanin fannin tarbiya ne.
2. Ba komai ne za mu yi wa yaro ba,ya kamata mu bar shi ya rika jarraba abubuwa da kansa don ya koya,misali yaro dan shekara biu yana kokarin sa takalmi ko riga ko safa kamata ya yi in bar shi ya jarraba idan ya iya falillahil hamd idan ba zai iya ba in yi kokarin koya masa. Amfanin barin ya jarraba shi ne zai koyi cewa komai akan iya shi ne da gwaji, idan ba a gwada ba ba za a iya gane an iya ko ba a iya ba,kuma hakan zai cire masa tsoron gwada yin abu bayan ya girma, saboda tun yana karaminsa ya san gwaji ba aibu ba ne hasali ma hanya ce ta koyo. Haka ma duk wani abu da zai yi yunkurin yi in dai abu ne mai amfani wanda yake taimaka masa wurin fahimtar wani abu a yi kokarin barinsa ya yi in yana bukatar taimako a taimaka masa ta hanyar tanadar masa abubuwan da za su taimaka masa ya fahimci abunda yake so ya fahimta,kawai dai sharadi shi ne ya zama abun ba wanda zai kai shi ga halaka ba ne,idan abun yana da hadari a yi kokarin kare shi daga hadarin.
3. A yi kokarin fahimtar da yaro kowa dan tara ne bai cika goma ba. Wato ya fahimci kowa yana kuskure,kawai ana son idan mutum ya yi kuskure ya yarda da kuskurensa kuma ya gyara.
Shi ya sa baa son in yaro ya yi abu ba, daidai ba a katsa masa tsawa ko duka kawai yaro ya wuce yana kuka ba tare ma da ya san me ya yi ba,abun da ake so a kwantar da hankalin a nuna wa yaro kuskurensa tare da koya masa yanda zai gyara kuskure idan ya yi.
Rashin fahimtar da yaro abunda ya yi ba daidai ba kuskure ne da koya masa hanyar gyara sai dai tsawa ko duka ya kan kashe wa masa sifar yarda da kai, zai tashi kullun yana mai zargi da kyamar kansa da ganin rashin amfaninsa ga alumma da jin yana da nakasu a rayuwa.
4. Ana son idan yaro ya yi abun kwarai a yaba masa amma kar a wuce gona da iri don wuce gona da iri yana haifar da sakamakon da ba shi ake bukata ba. Malaman tarbiya suna ganin an fi so a yabawa aikin da yaron ya yi ba shi yaron kan sa ba don kar ya sa masa girman kai da jin cewa shi wani ne. Misali na sa yaro ya yi shara abun da ya kamata in ce kai masha Allah yau sharar taka ta yi kyau ba in ce kai wane ka iya shara ba. Kuma ba a son yabawa ta zama kyauta ta kudi ko wani abu mai kima saboda hakan zai sa idan ka sa yaro ya yi abu ya fara tunanin za ka ba shi wani abu ko ya zama abunda yake yi saboda abunda za ka ba shi ne. An fi so ko ka masa addua ko ka dan shafa kansa ko ka rungume shi da dai sauran ire iren wadannan.

5. Idan zaa raba aikin gida to a raba da yaro sai a ba shi aiki gwargwadon shekarunsa da karfinsa. Kada a ce shi karami ne ba zai iya ba. Sa shi a cikin aikin gida zai haifar masa da jin kima da yarda da kai,ya kuma sa masa girmama halin taimakekeniya in ya girma.
6. Gujewa kwatanta yaronka da wani koda dan uwansa ne,saboda Allah ya halacci dabia da halayyar kowa daban. Yin hakan yakan haifar da kiyayya tsakani,misali a rika cewa yaro duba yayanka kullun na daya yake yi kai kuwa kullan na baya ka ke yi,to ka sani wannan ba hanya ce ta kwadaitar da shi ba sai dai ka sa kiyayya tsakaninsu don har kullun ji yake baya sonsa saboda ya fi shi,kamata ya yi ka fahimtar da shi amfanin murajaa da taimaka masa wurin yin ta da ba shi labarin mutane masu kwazo da himma har ya ji cewa shi ma ya kamata ya kara kwazo wurin karatu don ya samu sakamako mai kyau. Don haka mu guje kwatantawa tsakanin yaranmu don ba ya haifar da wani sakamako face na kiyayya.
Kundin tarbiya
Fatima Bello D/malam
16/9/2019

Comments
Post a Comment