GABATARWA

Gabatarwa

Allah madaukakin sarki a cikin kuraninsa mai tsalki ya siffanta mana yara yana mai cewa “المال والبنون زينة الحياة الدنيا” fassara “dukiya da ‘ya’ya su ne kawar rayuwar duniya.
Zamu tabbatar da haka ne idan muka yi laakari da irin farin ciki da tasirin da yara su ke bar mana a cikin zukatanmu lokacin da suke abubuwan ban dariya na nuna halin kurciya har dai lokacin da suke kanana. Mutum ba zai iya gane haka ba sai lokacin da ya nisanta da su.
Don haka ka sani cewa kyautar ‘ya’ya daga Allah niima ce baba da ya maka,ya zama dole ka yi aiki tukuru don dora wannan niimar akan hanyar da ta dace,hanyar da Allah yake so,don zai tambaye ka akan ta ranar kiyama.
Mai karatu biyo ni a hankali don samun haske a kan hanyoyin da suka dace ka dora yaranka a kansu don samun kyakkyawan iri da zaka yi alfahari da shi anan duniya kuma ka samu babban rabo a gobe kiyama.

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN TARBIYA(1)

HANYOYIN TARBIYA(4)

HANYOYIN TARBIYA(3)