HANYOYIN TARBIYA(2)
Karkashin dasa kyakkyawar akidah ga yaro,kamar yanda muka sani cewa son Allah yana tare da son Annabi (SAW) ne don haka kai mai tarbiya ka sani cewa dole ne ka cika zuciyar yaronka da son Annabi(SAW). Saboda son Annabi (SAW)yana cikin cikar imani. Annabi (SAW) ya ce"لا يؤمن احدكم حتى اكون احب اليه من والده وولده والناس اجمعين" fassara,"Imanin dayanku ba zai cika ba har sai na kasance nine mafi soyuwa gare shi akan 'ya'yansa da mahaifansa kai da ma mutane gaba daya. To amma ta wace hanya za mu bi mu dasa son Annabi(SAW)a cikin zukatan 'ya'yanmu.
1. Karantar da su tarihin Annabi(SAW) da yi musu bayanin cewa an aiko shi ne don fitar da mu daga duhun jahilci zuwa ga shiriya kuma shi rahama ne gare mu kamar yanda kurani ya yi bayani.
2. Fitar musu da halayen Annabi(SAW) daga tarihinsa da kurani da yi musu bayanin shi ne mafificin halitta don haka shi ne abun koyi a gare mu.
3. Yi musu bayani a kan muujizojinsa
4. Yi musu bayani a kan muamalarsa da yara da tausayinsa a gare su
5. Karantar da su irin soyayyar da sahabbai suke masa da girmama shi
6. Karantar da su hadisansa
7.koyar da su yawan salati gare shi(SAW)
Amma fa duk wannan zai kasance ta hanyoyi masu kwadaitarwa da kuma sa hikima a wurin isar da sakon ba kawai katantawa a fassara ba,kuma ya kamata a yayin isar da sakon a kula da shekarun yaro da hankalinsa ta yadda zai iya fahimta.
Suma sauran annabawa haka zaa fahimtar da yaro girmansu da bayani akan son Annabi (SAW) yana tare da son su.
Haka Sahabban Annabi (SAW),su ma a karantar da yaro tarihinsu da gwagwarmayar da suka sha wurin taimaka masa da bayani akan girmansu da darajarsu kamar yanda kurani da hadisai suka tabbatar.
Haka ma zaa ci gaba da koyar da yaro sauran rukunan imani sallah azumi yarda da kaddara da sauransu.
Mu hadu a fitowa ta gaba In sha Allah
Comments
Post a Comment