BUKATA TA UKU (2)
Hanyoyin da zan bi don in tabbatar wa yarona siafar yabo da karfafawa a cikin zuciyarsa: 1. Kula da kokarin da yaro yake yi komai karancinsa,kuma in kiyaye sosai duk abunda yaro ya yi na kwarai in nuna farin ciki akai da yabawa. Amma dai malaman tarbiya sun nuna aikin ake so a yaba shi kuma yaron a yabi kokarinsa. Misali yaro ya ci abinci bai zubar ba in ce masa masha Allah yau kam ba ka warwatsar da abinci a kasa ba hakan yana da kyau kuma ka yi kokari,kun ga nan na yabi aikin kuma na yabi yaron don na nuna ya yi kokari. Wannan yakan sa mishi farin ciki da kuma karfafa guiwarsa. Amma matsalar da ake samu a wajen iyaye ita ce mafi yawan lokaci anfi kula da laifukan da yaro yake yi sabanin kokarin da yake yi. Misali jiya ya ci abinci ya zubar kika yi ta fada da tada jijiyoyin wuya,yau kuma sai ya ci bai zubar ba kawai aka dauke kwanon aja wuce wurin ba tare da an ce komai ba. Don Allah akwai adalci a hakan. To wai ma ya zaa yi ya gane rashin zubarwar abu ne mai kyau. Wani yaron...