BUKATUN YARO DA SUKA SHAFI ZUCIYARSA
BUKATA TA FARKO
1. Yaro na bukatar kulawa(consideration) wannan yana nufin cewa yana so ya ji cewa shi ma mutum ne a cikin mutane,ayi masa muamala irin muamalar da ake yi wa manya,a saurare shi, a girmama shi, ayi shawara da shi,wannan zai sa ya ji cewa shi ma yana da muhimmanci a cikin mutane. Idan bai samu haka ba shi ya sa wasu dabiu za su bayyana gare shi saboda ya isar da sako ga manyansa cewa yana bukatar wannan sifar
Dabiun da suke bayyana ga yaro don isar da wannan sakon su ne:
- Rashin jin magana da gangan
- Barna, saboda kawai ki yo kansa
- kin cin abinci in ya san wannan zai bata miki rai
- kukan banza,don ya jawo hankalinki ki koma kansa
- Rashin kunya gaban mutane
- Karya da kirkiro labarai da ba su da kan gado
Hanyoyin da za ki bi don yaronki ya ji cewa kin ba shi kulawa:
- A samu lokaci kullun wanda zaa zauna da shi ayi labari da shi don ya samu fito da abubuwan da suke zuciyarsa da tambayoyinsa ba tare da tsoro ko kunya ba,yin haka zai sa ya saba da magana da ke da fitar miki duk abunda ke damunsa da asiransa ko bayan ya girma. Da yawa daga cikin iyaye sun fada cikin rashin sanin matsalar da yayansu suke ciki saboda tun suna yara iyayen ba su kula sun bude hanyar tattaunawa da hira da su ballantana su fahimci me ke cikin zuciyarsu.
- Ba shi 'yancinsa gwargwadon hankalinsa,ki bari ya zabi abunda yake ya shafi rayuwarsa ne in dai ba zai cutar da shi ba. Kada ki taba wakiltarsa a kan abunda ya shafe shi,bar shi ya dogara da kansa don abunda yaro yake bukata kenan.
- A raba aikin gida da shi gwargwadon girmansa da karfinsa,wannan zai sa ya ji cewa shi ma wani jigo ne a cikin family
- Ki rika yabon ayukan da yake yi na kwarai,an fi son a yabi aikin da yaro ya yi ba shi yaron ba, misali kai yau sharar taka ta yi kyau ba ki ce kai ka iya shara ba.
- kar ki taba bayyana laifinsa gaban baki, saboda comments da za su yi zai iya tsaya masa a zuciya har bayan ya girma
- ki zama mai alfahari da shi ko da yaushe da sa masa albarka.
Mu hadu a fitowa ta gaba In sha Allah.

Comments
Post a Comment