BUKATA TA UKU (2)


Hanyoyin da zan bi don in tabbatar wa yarona siafar yabo da karfafawa a cikin zuciyarsa:
1. Kula da kokarin da yaro yake yi komai karancinsa,kuma in kiyaye sosai duk abunda yaro ya yi na kwarai in nuna farin ciki akai da yabawa. Amma dai malaman tarbiya sun nuna aikin ake so a yaba shi kuma yaron a yabi kokarinsa. Misali yaro ya ci abinci bai zubar ba in ce masa masha Allah yau kam ba ka warwatsar da abinci a kasa ba hakan yana da kyau kuma  ka yi kokari,kun ga nan na yabi aikin kuma na yabi yaron don na nuna ya yi kokari. Wannan yakan sa mishi farin ciki da kuma karfafa guiwarsa.

Amma matsalar da ake samu a wajen iyaye ita ce mafi yawan lokaci anfi kula da laifukan da yaro yake yi sabanin kokarin da yake yi. Misali jiya ya ci abinci ya zubar kika yi ta fada da tada jijiyoyin wuya,yau kuma sai ya ci bai zubar ba kawai aka dauke kwanon aja wuce wurin ba tare da an ce komai ba. Don Allah akwai adalci a hakan. To wai ma ya zaa yi ya gane rashin zubarwar abu ne mai kyau. Wani yaron ma da yake da kaifin hankali zai fahimci matsalar ba wai zubar da abincin ne ba kawai ba kya son ya saki aiki ne musamman ma in shi a zai iya sharewa ba, kin san kuwa tunanin haka zai haifar masa da son kai tare da wasu dabiu da ke ba ki ma yi tunani akansu ba. Mu muke bata yayanmu da kanmu mu dasa mudu miyagun dabiu ba tare da mun sani ba kuma muna nan muna ta kurin muna ba su tarbiya.
2. Idan kika gaa yaro yana kokarin yin wani abu yi kokari ki taimaka masa da yaba masa da karfafa masa guiwa ko da kuwa bai iya ba. Ba don komai ba sai don hakan ya taimaka masa wurin ci gaba da yi din har y koya ya iya. Domin idan ba ki karfafa shi ba kika kwatse shi kika karbe daga hannunsa kika ce masa don Allah gafara kai komai ba ka iya ba,zai sa masa bacin rai da kunci ya kima karya masa guiwa ya hana shi koya saboda tsoron kar ace bai iya ba, kuma wannan yakan kashe wa yaro ruhin fasaha da kwazo. Idan ma kika ga yana ta yi bai iya ba kuma yana ta so ya iya ki karba ki koya masa maimakon kwatsewa da dizgawa.
3. Idan yaro ya yi abun kwarai to fa in zaki yaba dole fa ki tabbatar da yabon nan daga zuciyarki ya fito wato ya zama da gaske kike yi ba wai kawai irin kar ya ce ba ki yaba ba,aa yara suna da kaifin basira za su gane ba da gaske kike yi ba.
4. Kada a wuce gona da iri wurin yabon yaro musamman gaban mutane saboda wannan zai iya haifar masa da girman kai da alfahari.
5. Yabawa yaro ga abunda ya yi na kokarinsa a lokacin da ya yi abun kar ki yarda ki fita batun abun har wani lokaci sannan ki yi commen,misali yaro ya zana wani abu ya sheko da gudu yana murna yana jin dadi ya kawo miki don ganin kokarin da ya yi to ya kamata a wannan lokacin ki nuna appriciating naki da comment akai. Kada ki yarda ki kore shi ki ce masa ba ka ga ina aiki ba ko ina da baki ba aa sam don wannan zai karya masa guiwa.
Mun hadu a fitowa ta gaba In sha Allah

Fatima Bello D/malam
Kundin Tarbiya
9/11/2019

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN TARBIYA(1)

HANYOYIN TARBIYA(4)

HANYOYIN TARBIYA(3)