BUKATA TA UKU (1)


Yaro yana bukatar a rika yaba masa ana kuma karfafa shi. Mafi yawan iyaye suna ganin cewa yabon yaro yana sangarta shi,sai suke ganin yi masa fada da fitar da laifukansa gaban mutane yana kara masa hobbasa, shi ya sa za ka ga wasu iyayen sun kai karar yaronsu makaranta su kuma makaranta su hada masa assembly su tona asirinsa a gaban yara suna ga kamar hakan zai sa ya ladabtu to mu sani wannan sam ba hanya ce ta gyara ba kuma kuskure ne babba. Yaro yana so a rufa masa asiri. Sannan in ya yi abun kwarai a yaba masa a sa masa albarka hakan yakan kara masa karfin guiwa.
  Malaman tarbiya suna ganin cewa iyaye ne suke da dauri babba wurin gina yaro ta hanyar yabonsa da karfafa shi,hakan yakan kara masa self confidence. Idan kuwa har yaro bai samu wannan yabon da karfafawar iyayensa ba to zai masa tasiri can gaba in ya girma,zuciyarsa za ta yiwa kanta fighting don ta samarwa kanta wannan sifar da ya rasa. Misali za ka ga yana kokarin sayen abubuwa masu tsada koda kuwa ba hali ne da shi ba don ya karkato idon mutane a kansa saboda a rika yaba masa ana kambama shi saboda kawai ace shi ne,wannan yana faranta masa rai yakan maye masa gurbin gibin da ya samu na rashin yabo da karfafa masa guiwa daga wurin iyayensa. Idan muka lura kuwa za mu ga wannan siffar tana da yawa acikin alumma. To yanzu mun ji cewa rashin karfafa yaro da yaba shi akan daarsa da ladabinsa da ayukan kwarai da yake yi yana cikin dalilan da suke kawo waccan matsala da muka fada. Don haka iyaye ya kamata mu kula da wannan. Ba wai in rika yabon yaro akan hakurinsa ko ladabinsa bayan baya nan ba, aa a gabansa in fada, in sa masa albarka, in ta kama ma in masa kyauta ta musamman saboda in kwadaitar da shi akan dagewa akan wannan halin na kwarai da yake yi, kuma hakan zai taimakawa yanuwansa su yi koyi da shi.
  Akwai hanyoyi da ya kamata in bi don in tabbatar da wannan sifar da muke magana a zuciyar yaro saboda in kubutar da shi daga nemanta can gaba idan ya girma.
Mu hadu a fitowa ta gaba in sha Allah


Fatima Bello D/malam
Kundin tarbiya
9/11/2019

Comments

Popular posts from this blog

HANYOYIN TARBIYA(1)

HANYOYIN TARBIYA(4)

HANYOYIN TARBIYA(3)