BUKATA TA BIU
Yaro yana bukatar ya samu natsuwa da yarda: Iyaye suna yin wasu kurakurai a gaban yara wanda hakan yakan sa su cikin hali na rashin natsuwa da jin dadi da rashin yarda,daga cikin wadannan kurakuran akwai:
1. Matsalolin rayuwa da suke faruwa tsakanin iyaye ko yan uwa bai kamata ana bari yara suna ji ko gani ba. Amma matsalar da ake samu sai ka ga iyaye ba sa kula da wannan, ka ga uba ya fito tsakar gida gaban 'ya'ya yana ciwa uwarsu mutunci wata kil har da zagi,wannan yakan sa yaro cikin rashin natsuwa da jin dadi da rashin yarda da tsaoro,don haka ya kamata idan aka samu irin wadannan matsaloli ayi kokarin warware su ba tare da sanin yara me ke faruwa tsakanin iyaye ko yan uwa ba.
2. Ba da yaro reno na tsawon lokaci,wato ya kasance ba ya tare da uwarsa tsawon lokaci,wannan zai sa shi cikin rashin natsuwa da rashin yarda da tsoro musamman idan wurin renon baa kula da shi yanda ya kamata.
3. Rashin samun hanya tabbatacciya wurin muamala da yaro, a rika juya shi kamar kwallo,uwa ta ce aa uba ya ce eh ko akasin haka sai yaro ya rasa menene daidai a cikin maganar iyayen sai ya shiga cikin damuwa da rashin natsuwa. Ya kamata iyaye su yi yarjejeniya wurin tarbiyar yaronsu maganarsu ta zama daya akan yaronsu don ya gane inda zai dosa.
4. Sakaci wurin tarbiyar yaro yakan haifar masa da rashin saiti a rayuwarsa kuma wannan zai sa mutane su tsane shi wanda hakan zai haifar masa da damuwa da rashin natsuwa da yarda.
Hanyoyin da ya kamata in bi don samarwa yarona natsuwa da jin dadi da yarda:
1. Amfani da hanya ta tausayawa da natsuwa yayin muamala da yaro musammam idan ya yi laifi,wannan ba zai hana in yi masa fada ba amma idan zan yi masa fadan in yi cikin natsuwa ba tare da tada jijiyoyin wuya ba,kar in yarda in muzguna masa ko in dizga shi musamman a cikin mutane,in tuna cewa shi mutum ne yana da feelings.
2. In yarona ya yi kuskure in bi hanyar da ta dace in ladabtar da shi,hanyar da za ta taimaka masa don ya gyara kuskuren,kar in yarda in ladabtar da shi kawai don ya bata min rai ba wai don gyaran kuskure ba,saboda daman ana ladabtar da yaro ne don gyara ba don daukar fansa ba.
3. Kokarin samar masa abubuwan da za su faranta masa rai wadanda za su samar masa natsuwa irin kayan wasa masu amfani,kissoshi, da sauransu,amma fa a guji ba wa yaro waya da computer musamman barin sa a kansu lokaci mai tsawo haka ma kallace kallacen banza a gaban TV don hakan yakan bata masa kwakwalwa ya haifar masa da aladun banza.
4. Ya kamata gaba daya iyalin gidan su yi kokarin samarwa kansu yanayi na walwala da farin ciki saboda yaronsu ya samu natsuwa da jin dadi a cikin gidan. Kada a yarda a bari gida ya zama ba abunda ke cikinsa sai fada da duka duk wanda ya fi wani karfi ya buge.
5. Sanya dokoki a cikin gida wanda kowa zai sansu kuma dole ya bi su,saboda idan yaro bai fahimci dokan gida ba zai ta yin abubuwa ne barkatai ku kuma manya ku yi ta hana shi kuna fada da shi sai wannan ya haifar masa damuwa da rashin natsuwa.
6. Kokarin adalci wurin muamala da yaranku,kar a yarda a fifita wani akan wani,domin shi wanda yake an fifita wani a kansa zai shiga cikin damuwa da rashin natsuwa kuma hakan yakan haifar da kiyayya tsakanin yan uwa.
7. A yi kokarin janyo yaro a jiki da kuma kokarin fahimtar damuwarsa idan aka ga ya shiga cikin damuwa da rashin jin dadi da sakewa.
Mu hadu a fitowa ta gaba In sha Allah.
Comments
Post a Comment