HANYOYIN TARBIYA(4)
3.Tarbiyantar da yaro a kan kyawawan halaye: Lallai tarbiyantar da yaro a kan dabiu na kwarai yana daga cikin abunda addinin musulunci ya yi umurni da shi saboda muhimmancin hakan ga mutum da kuma rayuwar alumma. Samar da 'ya'ya na gari ya kan samar da ci gaba ga alumma da kuma samun makoma mai kyau ga wanda ya sifantu da su. Siffantuwa da kyawawan halaye abu ne mai girma wanda dalilin hakan Allah madaukakin sarki ya yabi Annabinsa(SAW) a kuraninsa mai tsalki inda yake cewa:"وانك لعلى خلق عظيم"fassara "lallai kana a kan halaye masu girma" wato kyawawan halaye. Haka Annabi(SAW) yana cewa a cikin hadisi:"بعثت لأتمم مكارم الاخلاق" fassara "an aiko ni don in cika kyawawan halaye". Wato kyawawan dabiu su ne babban sakon da musulunci yake dauke da shi. Shi ya sa yake daga cikin alamar musulmi na kwarai siffantuwa da halaye na kwarai. Addinin musulunci gaba dayan shi yana misaltuwa ne a cikin kyawawan dabiu kuma imani kansa yana bayyna ta hany...