Posts

KYAKKYAWAR MUAMALA BABBAR MU'UJIZA CE A WURIN TARBIYA

Kyayyawar muamalar da kake yi wa 'ya'yanka/ki tana haifar da babban alamari wurin tarbiyarsu, domin ita ce za ta taimaka wurin gina kyakkyawar alaka tasakaninka/ki da su. Malaman tarbiya sun tabbatar da cewa kashi 70 cikin 100 na rassan da ake concentrating a kansu wurin tarbiya ya tattara ne a cikin kulla kyakkyawar alaka tsakanin iyaye da 'ya'yansu. Duk lokacin da alaka ta yi rauni tsakanin iyaye da 'ya'yansu duk lokacin da aka samu matsala a wurin tarbiya. Mafi yawan matsalolin tarbiya da suke faruwa a alumma sakamako ne na raunin alaka tsakanin iyaye da 'ya'ya. Idan ka kyautata muamalarka ga 'ya'yanka lokacin ne za su fi mutuntaka kuma su daukeka mutumen kirki, ganin cewa  mutumen kirki ne a idonsu shi zai sa ka ga duk wani abu na kirki da ka ke yi suna kokarin koyi da kai a kansa. Idan kuma ka munana muamalarka gare su za ka ga suna gudunka kuma ba sa mutuntaka, koda kuwa ka ga mutuntuwa to a gaban idanunka ne a bayanka za ka sha mamaki...

BUKATA TA UKU (2)

Hanyoyin da zan bi don in tabbatar wa yarona siafar yabo da karfafawa a cikin zuciyarsa: 1. Kula da kokarin da yaro yake yi komai karancinsa,kuma in kiyaye sosai duk abunda yaro ya yi na kwarai in nuna farin ciki akai da yabawa. Amma dai malaman tarbiya sun nuna aikin ake so a yaba shi kuma yaron a yabi kokarinsa. Misali yaro ya ci abinci bai zubar ba in ce masa masha Allah yau kam ba ka warwatsar da abinci a kasa ba hakan yana da kyau kuma  ka yi kokari,kun ga nan na yabi aikin kuma na yabi yaron don na nuna ya yi kokari. Wannan yakan sa mishi farin ciki da kuma karfafa guiwarsa. Amma matsalar da ake samu a wajen iyaye ita ce mafi yawan lokaci anfi kula da laifukan da yaro yake yi sabanin kokarin da yake yi. Misali jiya ya ci abinci ya zubar kika yi ta fada da tada jijiyoyin wuya,yau kuma sai ya ci bai zubar ba kawai aka dauke kwanon aja wuce wurin ba tare da an ce komai ba. Don Allah akwai adalci a hakan. To wai ma ya zaa yi ya gane rashin zubarwar abu ne mai kyau. Wani yaron...

BUKATA TA UKU (1)

Yaro yana bukatar a rika yaba masa ana kuma karfafa shi. Mafi yawan iyaye suna ganin cewa yabon yaro yana sangarta shi,sai suke ganin yi masa fada da fitar da laifukansa gaban mutane yana kara masa hobbasa, shi ya sa za ka ga wasu iyayen sun kai karar yaronsu makaranta su kuma makaranta su hada masa assembly su tona asirinsa a gaban yara suna ga kamar hakan zai sa ya ladabtu to mu sani wannan sam ba hanya ce ta gyara ba kuma kuskure ne babba. Yaro yana so a rufa masa asiri. Sannan in ya yi abun kwarai a yaba masa a sa masa albarka hakan yakan kara masa karfin guiwa.   Malaman tarbiya suna ganin cewa iyaye ne suke da dauri babba wurin gina yaro ta hanyar yabonsa da karfafa shi,hakan yakan kara masa self confidence. Idan kuwa har yaro bai samu wannan yabon da karfafawar iyayensa ba to zai masa tasiri can gaba in ya girma,zuciyarsa za ta yiwa kanta fighting don ta samarwa kanta wannan sifar da ya rasa. Misali za ka ga yana kokarin sayen abubuwa masu tsada koda kuwa ba hali ne da shi...

BUKATA TA BIU

Yaro yana bukatar ya samu natsuwa da yarda: Iyaye suna yin wasu kurakurai a gaban yara wanda hakan yakan sa su cikin hali na rashin natsuwa da jin dadi da rashin yarda,daga cikin wadannan kurakuran akwai: 1. Matsalolin rayuwa da suke faruwa tsakanin iyaye ko yan uwa bai kamata ana bari yara suna ji ko gani ba. Amma matsalar da ake samu sai ka ga iyaye ba sa kula da wannan, ka ga uba ya fito tsakar gida gaban 'ya'ya yana ciwa uwarsu mutunci wata kil har da zagi,wannan yakan sa yaro cikin rashin natsuwa da jin dadi da rashin yarda da tsaoro,don haka ya kamata idan aka samu irin wadannan matsaloli ayi kokarin warware su ba tare da sanin yara me ke faruwa tsakanin iyaye ko yan uwa ba. 2. Ba da yaro reno na tsawon lokaci,wato ya kasance ba ya tare da uwarsa tsawon lokaci,wannan zai sa shi cikin rashin natsuwa da rashin yarda da tsoro musamman idan wurin renon baa kula da shi yanda ya kamata. 3. Rashin samun hanya tabbatacciya wurin muamala da yaro, a rika juya shi kamar kwallo,u...

BUKATUN YARO DA SUKA SHAFI ZUCIYARSA

BUKATA TA FARKO 1. Yaro na bukatar kulawa(consideration) wannan yana nufin cewa yana so ya ji cewa shi ma mutum ne a cikin mutane,ayi masa muamala irin muamalar da ake yi wa manya,a saurare shi, a girmama shi, ayi shawara da shi,wannan zai sa ya ji cewa shi ma yana da muhimmanci a cikin mutane. Idan bai samu haka ba shi ya sa wasu dabiu za su bayyana gare shi saboda ya isar da sako ga manyansa cewa yana bukatar wannan sifar   Dabiun da suke bayyana ga yaro don isar da wannan sakon su ne: - Rashin jin magana da gangan - Barna, saboda kawai ki yo kansa - kin cin abinci in ya san wannan zai bata miki rai - kukan banza,don ya jawo hankalinki ki koma kansa - Rashin kunya gaban mutane - Karya da kirkiro labarai da ba su da kan gado  Hanyoyin da za ki bi don yaronki ya ji cewa kin ba shi kulawa: - A samu lokaci kullun wanda zaa zauna da shi ayi labari da shi don ya samu fito da abubuwan da suke zuciyarsa da tambayoyinsa ba tare da tsoro ko kunya ba,yin haka zai sa ya saba d...

KYAKKYAWAR ZUCIYA A MARHALAR KURCIYA

  Kurciya ba za ta gushe ba tana nan a kan zama jigon alumma,su kuma yara suna nan a kan zamansu albarkatun kasa,idan aka yi tattalinsu a amfana da su,idan aka yi watsi da su alumma ta sha wahala.   Marhalar kurciya tana cikin mafi muhimmancin marhalolin rayuwar dan adam,dalilin haka  ne ya zama dole masu tarbiya su kula da bukatun wannan marhala musamman na zuciya.   Iyaye suna kula da bukatun yaro na abunda ya shafi cinsa da shansa,tufafinsa,karatunsa amma ba duk iyaye  ne suka  kula da me zuciyar yaro take bukata don ta zama lafiyayya ta yofinta daga munanan dabiu. Wa su iyayen sun kokarta don su biya wadannan bukatu na zuciyar yaro amma kuma sai suka samu matsala wurin fahimtar maanar wadannan bukatun,suka fahimci cewa yi wa yaro duk abunda yake so,in ya yi laifi ba zaa lurar da shi ba,ko me ya nema a ba shi,shi ne samarwa yaro kyakkyawar zuciya lafiyayya.   Wadanne hanyoyi ne ya kamata iyaye su bi don biyawa yaronsu bukatunsa na zuciya don ya ...

YARDA DA KAI(self confidence)

Yarda da kai,wata sifa ce da ya kamata iyaye su kula da ita yayin tarbiyar 'ya'yansu. Domin kuwa rashin samun wannan sifa tun yaro yana karami ya kan haifar masa da matsaloli da dama har bayan  girmansa. Rashin yarda da kai shi yake sa mutum ya rika tsoron jarraba abubuwa a rayuwarsa,tsoron magana cikin mutane,yanke hukunci idan abu ya same shi,yawan raki,rashin sanin ciwon kai,guduwa a kan abunda yake ya kamata mutum ya yi. Rashin yarda da kai ne yake sa mutum ya rika jin yana da nakasu,sai ya yi ta kokarin boye nakasin na sa da wasu abubuwa,shi ya sa kullun tunaninsa kar mutane su ce ya yi kaza,ko bai yi kaza ba. To wannan duk rashin samun sifar yarda da kai ne tun yaro yana karaminsa. Kadan daga cikin hanyoyin da suke gina sifar yarda da kai a wurin yaro lokacin da ake tarbiyarsa a shekarunsa na farko na rayuwarsa,domin gina rayuwar mutum tana dogara ne akan yanda aka yi muamala da shi lokacin yarinta. 1. Bawa yaro zabi akan abubuwan da suka shafi rayuwarsa,misali wata r...